Monday, September 26, 2016

Ban san shi ba 6-10

[7/10, 12:58 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  6
Yauma kamar kullum, da yamma duk suna zaune a falo, Minal na kwance kan chinyar ummanta, Nusaiba ce ta shigo ta dawo daga islamiya, sai cewa ta yi, "ke mahaukaciya! ki je waje ana kiran ki", aunty Hafsah tace "wai ke Nusaiba yayar taki kike cewa mahaukaciya dan bakida kunya ko?" Ta maka mata harara kamar manyan idanunta za su zazzago 'kasa, ita kuma ta murgud'a mata d'an 'karamin bakin ta, tace “toh ba mahaukaciyar bace ne? Kullum daga ihu sai kuka", Abbah ya daka mata tsawa “ke fitsararriya wa yake kiran ta a waje? Kuma kika sake kika sake kiran Minal da mahaukaciya sai na 6a66alla ki a gidan nan". Hajiya Ma’u ta jawo ta, “zo nan ‘ya ta kar ya miki illa, zai sauke haushin a kanki, toh ai ba ke kika haukatar musu da ‘yar ba”. Abbah ya sake daka mata tsawa, “wa yake kiran ta na ce?” Ta zun6ure baki, yaya Al-amin ne mana ya zo. Jin hakan ya sa Minal ta mi'ke da sauri ta je d'aki ta d'an gyara fuskarta, ta fito ta yi waje.
Al-amin shi ne saurayin Minal da ta ke so, d'an gidan aminin mahaifinta ne, Alhaji Salisu, wanda suka tashi tare da mahaifin nata tun suna yara, komai a tare suke yi, dan duk 'yan asalin jahar   Sokoto ne, kuma yanzu haka kuma a tare suke zaune a Abuja. Har anyi musu baiko da Minal kuma an kawo lefe, jira kawai ake yi Al-amin ya kammala wani course da ya ke yi a Malaysia ya dawo a yi auren su. Yanzu ma hutu ne ya dawo da shi.
Minal ta isa wurin sa da lallausar murmushin ta, duk da ta yi rama  ta yamutse kwana biyu, hakan bai hana fitowa da kyaun ta ba, ta isa da sallamar ta, ta ce “What a surprise my hubby, ashe kana gari?” Ya mayar mata da murmushi, babyna jiya na zo, ganin na kasa samun ki a waya, ba chat, ba komai, wannan ne ya d'aga min hankali, ya sa na tattaro na dawo  na ga meh ya ke damun masoyiya ta. Minal ta rufe fuska da zara zaran yatsunta, tace "I’m sorry habibinah, dole ce ta sa na ajiye duk wayoyina" , yace "dole kamar ya?"  Tace "muje chan garden mu zauna, sai na maka bayanin me yake faruwa" . Suka je suka zauna akan kujerun da ke cikin garden d'in, yace "ina jin ki babyna gayamin dalilin da ya sa kika ajiye wayoyin ki, kikamin mummunan horo na rashin jin sautin ki, da sanin ya lafiyar ki take". Zata fara masa bayani kenan sai aka kira wayar sa, ya d'aga, bayan ya gama wayar ne Minal tace, "wow hobby, muga wayar ka ta burge ni, harda kalarta mai kyau", yace "ko kina so ne na bar miki?" Tace "no sweetheart, waya da kake ganinta ri'keta a gareni ba 'karamin  tashin hankali ba ne" . Ta kar6i wayar tashi tana dubawa, sa'ko ne ya shigo a wayar tashi, wanda ya d'aga hankalin Minal, ya sa ta zare ido, wannan ko a mafarki taga wannan lambar zata ganeta, lambar da ke damun ta ce da sa'konni a kowane lokaci, ta mi'ke tsaye jikin ta na 'kyarma, hakan ya sa shima Al-amin ya mi'ke tsaye a rikice, lafiya Minal? Bakin ta na rawa ta ce hobby ina kasan mai wannan lambar? Sa'kon ta bud'e domin ta tabbatar da abinda take zargi. Ga abunda ta gani a ciki, (Zuciya ta tana zafi a duk lokacin da na ganki tare da wani MInal, zuciya ta tana suya a duk lokacin da na ga kina yiwa wani namiji murmushi Minal, Minal ina son ki san cewa ke tawa ce ni kad'ai, bana bu'katar ki tare da kowane d'a namiji. Ki kyaye wannan! Mai 'kaunar ki…). Wani ihu Minal ta saki ta saki wayar Al-amin ta fad'i, take screen d'in wayar ya tarwatse.
[7/10, 1:02 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  7

Al-amin ya du' ka ya d'auki wayar sa, ganin abinda ya sami wayar ya  ya harzu'ka.Ke Minal miye haka? Dama da gaske haukan da ake cewa kina yi gaskiya ne? Ji wannan asarar da kikamin Yanzu, kin san ko nawa na siyi wannan wayar da kika fasa min ita? Gashi ba’a ma samun kayan gyaranta a nan yanzu, Minal ta dafe kai tana kuka, “na shiga uku, wayyo Allah na, dan Allah ka rabu da ni, dan Allah dan son iyayen ka ka 'kyale ni, wallahi bana son ka, wallahi na tsane ka, dan Allah ka fita daga rayuwa ta ka barni na zauna lafiya". Al-amin baki bud'e yake kallonta, lallai Minal kin haukace, kuma ni ya kamata na ce na fasa auren ki, dan wallahi bazan iya rayuwa da mahaukaciya ba. Ya juya zai wuce, Minal ta bi bayan shi da gudu, Al-amin ka tsaya ka saurare ni, wallahi ba da kai nake yi ba, da shi nake yi, dan na san yana gani na, kuma yana ji na, da shi nakeyi, wallahi bana son sa, wallahi bana 'kaunar sa, yanzu ya turomin sa'ko a wayar ka, Al-amin ya girgiza kan sa, yace "waye ne  Minal?" Tace "BAN SAN SHI BA" . Tsaki ya ja, you are sick Minal, kina bu'katar a kaiki psychiatiric hospital dan a duba 'kwa'kwalwarki dan kin samu ta6in hankali, Allah ya baki lafiya, amma ni bazan iya auren mahaukaciya ba. Ya shiga motar sa ya ja ya barta a nan tsaye tana ruzgar kuka.
Da gudu ta koma cikin gida tana ta kuka ta fad' a kan ummah, tana fad'in "shikenan ummah ya raba ni da Al-amin, Abbah shikenan ya raba ni da Al-amin, Abbah Al-amin ya ce bazai aure ni ba, ka je ka bashi hakuri, Abbah ina son Al-amin bazan iya rabuwa da shi ba". Take zufa ya karyowa Abbah, ya mi'ke ya fara neman wayar Al-amin, Tambayar sa yake yi, me ya ke faruwa tsakanin sa da Minal? Al-amin yace "Abbah gaskiya ku yi hakuri bazan iya auren Minal ba", Abbah cikin tsananin damuwa yace "meh ya sa Al-amin?" Yace "bata gaya muku haukan da tayi min bane Abbah? Gaskiya ni bazan iya auren mahaukaciya ba Abbah, kuje ku nema mata magani kawai". Ran Abbah ba 'karamin 6aci ya yi ba da kalaman Al-amin, amma ganin yanda Minal ke kuka a kan sa, shi ya sa ya dake, yace "toh shikenan zan je in samu Abban ka da zancen dan ba za ku maida mu dattijawan banza ba", ya kashe wayar ya goge gumin da ke goshin sa, yace "Minal daina kuka, yanzu zan je in samu Alhaji Salisu mu yi maganar, Al-amin bai isa ya watsa mana kasa a ido ba". Yace "Shahid ya tashi su tafi gun Alhaji Salisu", ummah da Hafsah ne kawai ke ba Minal ha'kuri akan ta yi shiru komai zai daidaita, yayin da Hajiya Ma’u ke zaune tana tsefewa Nusaiba kan ta, tana ‘yan wa'ke-wa'kenta, a ciki tana jefa musu habaici. Ita ko ja’irar ‘yar tata ta san meh take nufi, sai dariya take kwasa abinta. A haka Hajiya Kulu ta shigo ta same su, ita ma ta zauna tana jajantawa Minal, da zancen Zainab da Shahid ta zo, amma kuma ganin yanayin Minal ya sa ta bar zancen, duk da Zainab d'in ta tabbatar mata dama chan ta dad'e da soyayyar Shahid a zuciyar ta, yawan zuwan da take yi gidan su Minal d'in dama duk dan ta ganshi ne, jin hakan ya 'kara wa mahaifiyarta 'kwarin guiwa, amma ganin matsalar Minal ta san ba wanda zai saurari zancen ta kaf gidan, dole ta ha'kura har zuwa lokacin da hankalin kowa ya kwanta.
[7/10, 1:04 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  8

Abbah kuwa da Shahid sun fita zuwa gidan Alh. Salisu, Suka ci sa’a kuwa yana nan, bayan sun gaisa ne Abbah ya fara magana, Alh. Salisu ya dakatar da shi, “nasan abinda ya kawo ka bai wuce zancen Al-amin da Minal ba, dama tun da dad'ewa nake jin 'kananun maganganu akan ‘yar taka ta samu motsuwa, amma na toshe kunne na tunanin zancen mutane ne kawai, amma yau Aminu ya tabbatarmin da a gabansa ma haukar tata ta tashi, har ta sa shi asarar tsadaddiyar wayar sa, kuma ya tabbatarmin da cewa shi bazai iya auren mahaukaciya ba, kuma Alhaji Abbah kafi kowa sanin hali na, kasan a tsari na ba matsawa a rayuwar ‘ya’ya na, dan haka na goyi bayan Aminu, kawai kaje ka nemawa ‘yarka magani, Allah Ubangiji Ya bata lafiya. Ba Abbah ba, har Shahid wad'annan maganganu sunyi matu'kar 6ata masa rai, Shahid ya mi'ke a fusace yace "Abbah tashi mu tafi, ai wannan chin fuska ne. Abbah ya mi'ke jiki a sabule, yace "Alh. Salisu kwata-kwata ban yi tunanin haka daga wurinka ba, na dauka zumunci da 'kaunar da take tsakanin mu ta wuce komai, ko da gaske ne ‘yata hauka take, ban d'auka kana d'aya daga cikin mutanen da za su guje ni da iyali na ba". Nan mahaifiyar Al-amin Haj. Saratu da take  la6e tana jin abinda ake yi, sai ko ta yi kutsul ta fito, tace, “Alhaji mu sai mu rufawa ‘yar taku asiri mu chutar da namu yaron? Sanin kan ka ne zaman mai hankali da ta6a66e ba abune mai yuwa ba, ranar  da haukar tata ta  tashi Allah kaid'ai ya san abinda zata masa, toh mu gaskiya ba zamu yarda ba, dole ne a fasa wannan aure”. Alhaji Salisu ya mi'ke, “Kayi ha'kuri Alhaji Abbah, amma ni a gaskiya ban had'a komai da farin cikin ‘ya’ya na ba, dan haka bazan tilasta yaro na auren mahaukaciya ba”. Wani zugi Abbah ya ke ji a zuciyar sa a duk lokacin da aka kira Minal d'insa da mahaukaciya, hakan ya sa Abbah ya 'kara harzu'ka ya d'agawa Alh. Salisu hannu, cikin tsawa yace, "nagode Allah da ya nuna min irin 'kaunar da kake min a yau, nagode Allah da ban aurar da ‘yata a wurin da ba za’a iya tsaya mata ba komai ya same ta, Alh. Salisu ina so ka san wani abu, daga yau zumuncin da yake tsakanin mu ya 'kare, ba wai ina nufin na huld' ar da ta ke tsakanin 'ya'yanmu ba kawai, a'ah dangantaka komai, ta kasuwanci da duk wata mu'amala da take shiga tsakanina da kai da iyalina, yanda kace ba zaka tilasta 'ya'yanka ka chutar da su ba, haka nima ba zaka 'kara ra6ata ba, dan ban yarda dakai ba, dangantakar da take tsakaninmu tin kan musan zamu sami wasu 'ya'ya a duniya ta 'kare daga yau, dan nima bazan iya zama da ma'kiyi na ba, kuma ma'kiyin iyalina, bazan iya huld'a da wanda yake gudun had'a zuri'a dani ba, kawai dan wata lalura ta sami 'yata, kuma minal ba hauka take ba, wata lalura ce ta had'u da ita, kuma soon inshaAllahu zamuyi maganinta, koda kuwa duk abunda na mallaka a duniya zai 'kare", ya juya fuuuu ya fice, alhj salisu ji yake kamar ya ruga da gudu ya kamoshi ya bashi ha'kuri, amma yana gudun yayi abun kunya a gaban iyalinsa, tabbas yasan rashin alhj abbah a harkokinsa ba 'karamar asara zai tafka ba, dan alhj abba ya toshe masa 'kofofi da dama, amma yanzu bari ya barshi, daga baya ya bishi ya lalla6ashi su daidaita.
[7/11, 8:43 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  9
Alhj abba da shahid na fita hjy saratu itama ta kwashi direba ta nufi gidan su minal d'in tana zage-zage, tana fad'in dole ne naje na kwaso dukiyar d'ana da take gidan, kwandala bazan barmusu ba, zan nuna musu ba sai dasu zamu iya rayuwa ba, alhj slisu shidai jinta kawai yake, dan yasan da bazar alhj abba yake taka rawa.
   Tun a hanya abbah yace "shahid na baka dama duk wata share (hannun jari) da kasani da sunan alhj salisu a kamfanina kasakasu a kasuwa ka siyar da su, dama ai duk ni na siya masa su, amma wlh daga yau ta 'kare ba ni ba shi", shahid yace "angama abbah, dama ni na tsani mutumen wlh, zai gane shi ba komai bane"  da haka suka isa gida ko wannen su huci yake kmar tsohon kumurci kan tsananin 6acin rai. Minal tana ganinsu ta taso da gudu tayo wurin abbah tana fad'in "abbana al'amin ya hakura ko? Abbana al'amin bai fasa aurena ba ko?" abba yayi shiru hawayen ba'kinciki ne suka zubo masa ba tareda ya sani ba, yayi sauri ya share, ya bud'e baki zaiyi magana kenan, sai ga hjy saratu ta fad'o gidan ba ko sallamah, hakan yasa ummah da hjy kulu suka mi'ke tsaye cikin hanzari, hjy kulu tace "haba hjy saratu, ai dai ko da meh kika zo bai dace ki fad'owa mutane gida ba ko sallamah ba", bud'ar bakinta sai cewa tayi "SALLAMAH AI ADDU'AR NEMAN AMINCI CE, NI KUMA BA AMINCIN NE YA KAWO NI BA" baki suka saki suna kallonta cikin mamaki, tace "ba tare da 6ata lokaci ba inason a tattaromin duk wani Abu da kukasan d'ana ya kawowa wannan mahaukaciyar yarinyar, wlh 'kwandala kuka 6oye bamu yafe ba", take minal ta gano abunda ke faruwa, cikin sauri taje ta du'ka gun hjy saratu tace "momy dan Allah kuyi hakuri karku rabani da al'amin" wata dalleliyar harara ta mako mata, tareda cewa " ki d'aga ki bani wuri kar na hankad'eki, yarona bazai auri mahaukaciya ba wlh, saidai mu nemo masa dalleliya mai kyau da lfy ya aura amma ba ke ba"  ummah ranta yakai 'kololuwar 6aci tazo ta d'ago minal daga 'kafafun hjy saratu, minal ta fara tirjewa tana kuka, ummah ta daka mata uwar tsawa take ta nutsu, tace " hjy kulu muje ki tayani kwaso kayan, hafsah ma ta bisu, take suka kwaso kayan lefen minal da duk wani abu da suka San al'amin ne ya siyowa minal suka jibge mata, handkerchief wannan idan hfsh ta gayawa umma na al'amin sai an ciro shi, hjy saratu ta shiga binciken kayan taga wai koda an cire wani abun, ammma ga mamakinta komai yananan kamar yanda aka kawo, kayan gani ma tayi kamar 'karosu akayi.
'dago kanta da zatayi nusaibah ta watso mata kayan chocolate d'inda al'amin d'inne yake kawo mata idan yazo, harda juices, wani kwalin ma har ta fasashi duk ya tarwatse a jikin hjy saratu, Baki bud'e hjy saratu ke kallon nusaiba, ita kuma ta ri'ke kwankwaso tana jijjiga, tace " hajiya ga tsiyarku nan ku kwashe ku tafi, yayata zata iya zama mahaukaciya amma kunsan cewa dubun wannan kayan munfi 'karfinsu, Allah na tuba ai duk munsani ma da kud'in abbanmu aka siyi kayan, ko mijinki ba a wurin abbnmu yake maula ba? Amma dukda haka mu ba matsiyata bane ku kwasa ku tafi, idan ma banda kaddara meh aunty minal zatayi da yaya al' amin? Keda ganin fuskarsa ma kinsan shaye-shaye yake, kuma kowa ya sani d'an iska ne mata yake bi, nasha ji mommy na tana fad'a amma nayi shiru dan tace kar na fad'a, amma yau ya zama dole na fad'a dan bazaiyu ki shigo har cikin gidanmu ki ci mana mutunci ba, dan haka ga gayyar tsiyarku nan ku kwasa, ta fara d'ibar kayan tana wurgawa a waje, wasu ma 'kafa take sakawa tana ball da su, duk da tsanar rashin kunya da rashin mutuncin nusaiba da kowa yayi, yau ba wanda yayi 'ko'karin hanata, sai ma murna da sukayi yau ta tsayawa 'yar uwarta, ashe dai kowa da ranarsa, ko marasa mutunci ma da ranarsu, hjy saratu duk rashin mutunci da ta zo dashi, sai gashi tayi mus, mamaki ya kasheta yanda 'yar 'kan'kanuwar yarinya ta mata tatas ta kasa cewa komai, a haka cikin borin kunya ta kwashi kayan ta fita.
[7/11, 10:20 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL ,
       💖💞💝
    Ban yarda wani ko wata ya kwashe ko ya juyamin da labari ta kowacce irin hanya ba, duk wanda yayi haka wallahi Allah ya isa, ban yafe masa ba, kuma ko meh na masa shi ya ja wa kansa.
      
           Page  10

Tana fita hjy ma'u ta kwashe da dariya, Ana cewa 'yata 'yar iska ce, mara mutunci yau gashi ta tsayawa mahaukaciyar 'yarku, meh yasa yau ba wanda ya kwa6eta?ke zo nan nusi na er albarka, taje da gudu gun mamanta tana dariya, yau tayi abun kirki har abbah bai mata tsawar da ya saba ba.  Hajiya ma'u ta ci gaba " kuma mudai kaf danginmu ba muyi gadon mahaukata ba, bamuda mahaukaci ko d'aya saidai ko idan achan ta d'auko, ummah maganar ta mata zafi dan tasan da ita take yi, ta mi'ke tace " ma'u meh kike nufi? Kina nufin a dangina kenan minal tayi gadon hauka kenan? Tinda dai nice bare a cikinku, ma'u tayi dariya tace " kinji na ambaci sunanki hadiza? Dama dai ance mai kaza a aljihu baya jimirin asss". Abbah dai zuciyarsa a chunkushe take yama kasa che musu komai, ga uban kukan da minal take yi da yake 'kara 'kona masa zuciya.
   Shahid ne yazo gun minal d'in ya du'ka yace " 'kanwata kalleni, ta d'aga idonta da sukayi jajir ta kalleshi,  yace ki daina kuka, ke ba mahaukaciya bace, munsan kinada hankalinki, kuma zamuyi maganin matsalarki inshaAllah, kuma ki daina d'aga hankalinki akan al'amin, Sam bai dace da ke ba, kuma baya 'kaunarki, dan idan yana sonki da gaskiya minal duk halin da kika shiga bazai guje ki ba, masoyin gaskiya baya gudun masoyinsa duk tsanani duk wuya, dan haka ki yrda al'amin baya sonki ki daina 6ata hawayenki akan shi, wani hanin ga Allah baiwa ne, kina zaune zaki ga Allah ya Miki sauyi da mafi alkhairi, mai sonki da gaskiya, ki dage da addu'a kawai kinji 'kanwata? Gyad'a masa kai tayi tareda murmushi dan tasan gaskiya ya gayamata, ta d'ago tace " abbah ummah, kuyi hakuri na d'aga muku hankali, nasa anci mutuncinku, inshaAllah zanyi iya kokarina naga na cire al' amin daga zuciyata" .  Abbah ya sauke wata ajiyar zuciya ya dafa kafad'ar shahid, dan yasan maganganunsa ne suka sa minal ta ha'kura, yace " yace thanks son, ka tashi ku fita da 'kannenka ku zaga gari, kuje shopping da shan ice cream, Nusaibah ta taso, abbah nima dani za'aje shan ice cream d'in ko? Tinda dai yau nayi abun kirki, dariya abbah yayi kawai yace " je ki shirya 'yar momynta, kema aje da ke, suka tashi sukayi ciki domin su shirya, shima abbah yace zaije ya d'an watsa ruwa ya huta, ya wuce ciki.

   Hajiya kulu ta dubi hajy hadiza tace " ni ko hjy hadiza anya ba hannun kishiyarki a lamarin minal? Ki duba fa kiga, 'karara take nuna farincikinta akan abunda yake faruwa akan minal, hjy hadiza tace " hmmm kulu kenan, nasan ma'u sarai, nasan abunda zata iya da wanda ba zata iya ba, nasan ta tsani yanda taga abban minal yake sonta, amma kuma bata 6oye tsanarata da hasadarta, a bayyane take komai nata, ita dai ki barta da habaice-habaice, amma gaskiya bana tunanin wai da sa hannunta a lalurar minal, kuma kinji annabin rahma yace  "  AZZANU ZAMBUN WALAU KANA HAKKUN (ZATO ZUNUBI NE KO DA YA ZAMA GASKIYA)"  dan haka wlh har ga Allah bana zarginta, duk wani wanda yake nufinmu da sharri ina ro'kon Allah da ya mayar masa da mugun nufinsa,  hjy kulu tace  " amin, amma gaskiya hadiza zuciyarki tanada kyau, Allah yasa mu dace" , ta mi'ke da niyar tafiya, hjy hadiza tace hajiya kulu kar kiga kamar na 'kyale zancen shahida da zainab, Wallahi ba mantawa nayi ba, matsalar nan ce ta minal ta samu a gaba, amma inshaAllah da komai ya lafa zan shigo da zancen",  hjy kulu tace " karki damu kanki hadiza, Wallahi na fahimta,  Allah dai yasa mu dace". Sukayi sallamah ta fita.

BAN SANSHI BA 1-5

[7/10, 12:00 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  1

Tafe take cikin sauri tana waigen bayan ta, karar shigowar sa'kon waya da ta ji, shi ya kara sa hankalin ta ya tashi. Tsayawa ta yi, hannu na kyarma ta bude sa'kon, take kanta ya buga ta kuma kara firgita. Ga abunda ta gani a ciki (ki tsaya ki yi tafiyar ki tsaf mai daukar hankali, bana gajiya da kallon ki, ki daina takun sauri kada ki illatamin kan ki, kar ki manta, a duk inda kike, ina tare da ke. MAI 'KAUNAR KI… Hannunta ta dora a kai zata 'kurma ihu, yaya Shahid ne ya daka mata tsawa, WAI KE WACE IRIN MAHAUKACIYA CE MINAL? Tun dazu nake bibiyar ki a baya ina miki horn amma sai zabga uban sauri kike, anya Minal wannan rayuwar zata fishshe ki kuwa? Hannu ta dora a kai, yaya na shiga uku, Wallahi aljani ne, duk inda na shiga sai ya bini, komai nake yi yana gani na, kuka take ba tsayawa harda tsalle, kuma wallahi yaya BAN SAN SHI BA. Yaya Shahid ya ja dogon tsaki, wai wannan wace irin rayuwa ce? Bana gaya miki ki chanja layi ba? Tace wallahi yaya wannan na bakwai ke nan, shiru ya yi, Bani number din na kira, kira yake a kasha, wani sabon kukan ta dasa, yaya kullum number a kashe amma kuma kullum sai an yi min text da ita. Yaya Shahid yace yi shiru haka Minal, zo mu tafi gida. Ya ja hanunta ya saka a mota ya na girgiza kai, wannan waye yake nema ya zautar masa da ‘yar kanwar sa? Koma waye za suyi maganin sa.

WACECE MINAL?
Suna na Aminah Abbah Khaleel, amma anfi kira na da Minal Abbah Khaleel, yayin da qawaye na da classmates dina suke kira na da Minal Abbah kawai. Mahaifi na dan asalin jihar Sokoto ne, amma aiki ya kai shi birnin tarayya (Abuja) inda muke zaune. Mahaifiyata sunan ta Hajiya Hadiza, ni kad'ai ta Haifa, daga nan haihuwa ta tsaya mata, Wannan ne ya sa dangin mahaifina suka tilasta Abbahna ya auro ‘yar uwarsa, Hajiya Asm’au wacce ita ma Nusaiba kawai ta haifa daga nan haihuwa ta tsaya mata, hakan  ya sa mutane suka dinga cewa abun daga abbanmu ne, kowace mace ya auro daga ta haihu d'aya kuma shikenan, gashi baya da magaji, wai tinda bayada d'a namiji. Shekara bakwai ne tsakani na da Nusaiba, yanzu ina matakin farko ne a jami’ar Abuja (100 level) inda nake karatun ilimin kimiyya na na’ura mai kwakwalwa (Computer Science) yayin da Nusaiba take aji daya na karamar sakandare (JSSI).


WAYE SHAHID?
Yaya Shahid d'an 'kanen mahaifina ne, da yake mahaifin su bai yi wani zurfi a karatun boko ba, ya riga mahaifi na aure, shiyasa duk 'ya 'yansa suka girmemu, yaya shahid ne babba shekarunsa ashirin da bakwai yanzu a duniya, yana aiki ne a kamfanin abbah na, shi yake kula masa da dukkan dukiyoyinsa, yayinda aunty hafsah take bi mishi, itama tana matakin 'karshe ne a jami'ar abuja, yayinda take karanta mass communication.
  Mahaifinsu shahid 6ata yayi ba' a san inda yake ba, annemishi a ko'ina an rasa, tin yaya shahid nada shekara goma sha bakwai a duniya, wannan ne yayi sanadiyar sakawa mahaifiyarsu hawan jini har ta rasa ranta, daga lokacin ri'konsu ya dawo hannun abbanmu.
[7/10, 12:39 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  2

CIGABAN LABARI
A hargitse ta shiga gidan su, mahaifiyar ta Hajiya Hadiza da kawarta Hajiya Kulu suna zaune a falo suna fira, Minal ta fad'o falon kamar wadda aka koro ba ko sallama, da gudu ta wuce d'akin ta tana kuka, Hajiya Kulu ta kalli Hajiya Hadiza ta ce me ke faruwa da Minal ne? Yarinya mai nutsuwa da hankali amma yau ta shigo gida ba ko sallama, kuma ko ta gaida mu? Kuma na lura da bawai dan bata ganmu bane, Kafin Hajiya Hadiza ta yi magana sai ga Shahid ya shigo da sallamar sa, suka karba masa, ya rusuna ya gaida su, Ummah tace niko Shahid me ke damun kanwar taka ne? Ya dukar da kansa cikin nutsuwa ya fara magana. Ummah wallahi matsalar bata wuce wa’yannan sakonni da take samu a wayar ta ba kullum, kuma ta rasa gane waye, ni kaina bincike nake amma na kasa gane ko waye, amma wallahi ummah ko ma waye na yi alkawarin duk ranar da dubun sa ta cika sai ya raina kanshi. Hajiya Kulu ta ce niko Hajiya Hadiza anya yarinyar nan ba gamo ta yi ba kuwa? Tun lokacin da kika gayamin matsalar yarinyar nan kuma na yi nazari sai naga kamar aljanu ne kawai ke son wasa da hankalin ta. Amma ki bari zan yi ma wani malamin su Zainab magana naga yana rukiyya, sai ya zo ya mata. Hajiya Hadiza cike da tsananin damuwar abinda ke damun ‘yar ta kwaya daya tilo, ta ce bakomai Hajiya Kulu, Ki yi masa magana kawai, ni kaina matsalar yarinyar nan a kullum da ita nake kwana nake tashi, da chan na yadda da zancen mahaifin ta da yake cewa shirmen ta ne kawai mu kyale ta, Amma yanzu lurar da na yi yarinyar nan ba ta da sukuni a ‘yan kwanakin nan ya sa nima na fara shiga damuwa. Shahida ne ya mike ya ce ummah ni zan fita, ta ce toh ka dauki abincin ka gashi nan a kan dining, ya je ya dauka cikin girmamawa ya musu sallamah ya fita. Hajiya Kulu ta ce niko Hajiya Hadiza da za ki yadda da mun hada zumunci, auren Shahid da Zainab ta wuri na, dan yaron natsuwar sa ta yi min, na yaba da hankalin sa. Hajiya Hadiza ta ce duk da yaran zamanin nan, ba'a musu katsalandan a rayuwa, yaronnan ba ni na haife shi ba, amma na yar da da shi da natsuwar sa, yana ban girma tamkar ni na tsuguna na haifeshi, na tabbata bazai watsa mana 'kasa a ido ba, karki damu zanyi masa maganar. Hajiya Kulu ta mike ta ce zata tafi, tare da ro'kon Hajiya Hadiza da ta yi ma Shahid zancen Zainab, Nan suka yi sallamah ta tafi a kan za ta zo da mai rukiyya zuwa gobe.
Minal kuwa tun da ta fad' a d'akinta maida 'kofa ta rufe tana kuka, da ta gaji ta yi shiru dan kan ta, har wani wahallalen bacci ya yi gaba da ita, Ranar dai a ta' kaice bata bud'e 'kofar d' akin ta ba, ko abinci bata samu damar ci ba, Ummah da Aunty Hafsah sunyi-sunyi da ita ta bud'e kofar, ta'ki, Dole suka ha'kura suka 'kyale ta.
[7/10, 12:41 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  3

Tun bayan ta yi sallar asuba ta tsaya tana azkar na safe da karatun Al-Qurani, ta du' kufa da addu’a na Allah Ya shiga tsakanin ta da ma kowaye ke son ya zautar da ita, domin tun abin baya damun ta, yanzu ya hana ta sukuni. Bayan ta gama ne ta tashi ta shiga wanka ta fara shiri domin tana da lecture wanna ranar. Ta gama shirn ta tsaf, ta d'auko kayan ta ta fito waje, ta samu iyayen ta Alh. Abbah Khaleel, Hajiya Hadiza, da Hajiya Asma’u, Nusaiba kuma tana gefe, yaya Shahid da aunty Hafsah, duk suna kan dininig suna karyawa. Ta matsa ta gaida kowa cikin fara’a suma kowa ya kar'ba mata da fara’a. Abbah ya ce Minal d'in abban ta zonan kusa da ni ki zauna, ta je kusa da shi ta zauna tamkar ta shige jikin sa, Hakan ya sa Hajiya Asma’u ta ja wani gwauron tsaki, dan ta tsani yanda Alhaji yake nuna ya fi son Minal a kan ‘yar ta Nusaiba. Ba wanda ya kulata, domin idan da sabo, kowa ya saba dan halin ta. Abbah ya ci gaba, Minal d'ina shine jiya kika ki fitowa ki gaida ni ko? Ummahn ki ta gaya min tunda kika dawo makaranta baki fito ba, Ta ce ba komai Abbah na, kawai bana jin dad'i ne. Abbah ya ce, "kin san kuwa rashin ganin ki nima da zazzabi na kwana ko?" Hakan ya sa kowa ya yi dariya. Hajiya Hadiza ta ce "haba Alhaji ka daina fad'in haka mana" . Abbah da kan sa ya zuba ma Minal abin kari, ya ce Minal din Abbahnta ci abincin ki kar ki kula da umman ki, kishi ne yake damun ta. Hajiya Asma’u ta mi'ke tana sabbatu, haba! mutum kullum sai biyewa 'karamar yarinya, idan wani bai san ‘yarka bace ai ace wannan karuwarka ce, haba, son ‘ya hauka ne? A gaban ‘ya’yanka ka dage kana wani tarairiyar yarinya kamar ‘yar goye? Ta ce wa Nusaiba tashi muje direba ya wuce da ke autata, ko ba’a son ki dole ne a ganki. Nusaiba ta mi'ke zata wuce, Abbah ya daka mata tsawa, KE DAWO NAN KI KARASA BREAKFAST DINKI!!! Idan kika d'aga daga nan sai na 6alla ki. Ta dawo ta zauna tana zum6ura baki, daddy tunda ni baka son gani na ai gwanda na tafi, Shahid ne ya buge mata baki, ke gaki ‘yar 'karama se shegiyar tsiwar tsiya. Hajiya Ma’u ta 'kufula dan Alhaji da Hajiya Hadiza da ta so su kula ta, ba wanda ya kula ta, sai ta fara saukewa a kan Shahid, ta zage shi tatas. Kai d'an ri'ko ka zo ka fi masu gida sakewa harda dukan ‘yar masu gida, Aunty Hafsah ta je  ta maida mata amsa, Shahid ya d'aga mata hannu akan ta yi shiru ta 'kyale ta. Abbah ne ya mi' ke, Ma’u duk tsiyan da za ki yi zan iya 'kyale ki, amma bana son kina ta6a min yarana, Shahid da Hafsah da Minal da Nusaiba, duk d'aya suke a wuri na ba babanci, ‘ya’yan d'an uwana ne, uwa d'aya uba d'aya, dan haka ba suda bambanci da ‘ya’yan ciki na. Ke a kullum burin ki bai fi ki ga kin raba min kan ‘ya'yana ba, ‘yar ki da kike fad'in ba’a son ta, ki yi 'ko' kari ki koya mata tarbiyya, ita ce 'karama a gidannan amma rashin kunyar ta ya girmi kowa a gidannan, kuma duk lokacin da za’a yi mata fad'a ko a kwa6eta, bakya so a ta6a ta, to iya ‘yar gwal ce da ba za’a yi mata fad'a ba? Duk nawa Nusaiba take? Amma bata ganin girman kowa. Toh ya kamata ki chanja hali dan ki koyawa ‘yar ki tarbiyya yanda za ta girmama na gaba da ita, sannan sai a so ta. Nusaiba ce ta mi'ke, Mommyna mai so na muje nagama, na kuma gaji da jin Abbah yana miki ihu kamar wata 'karamar yarinya, kodai a so mu ko kada a so mu dole ne a ganmu, ba yanda za’a yi da mu, ita ‘yar da aka fi so ai gashi nan neman haukacewa take. Minal ta mi'ke a fusace zata janyo Nusaiba, Nusaiba ta ruga da gudu ta fita gidan. Hajiya Ma’u ta yi murmushi, na gode Allah da Ya ban ‘ya mai hankali, tun tana 'karama bata son ta ga ana cin zarafin mahaifiyar ta, ta wuce ta barsu da mamaki. Abinda Nusaiba ke yi ba wanda zai ce wai shekara goma ce, rashin kunyar ta bata ragawa kowa, har uwar tata idan ta tashi sai ta mata tas.
[7/10, 12:50 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  4

Shahid ne ya katse shirun da cewa " 'kanawata idan kun gama ku same ni a waje na sauke ku a makaranta" . Ya mi'ke ya fita, aunty Hafsah ma ta mi' ke ta yiwa su ummah sallama, Minal ma ta gama, sai  ta tsaya tana kwashe kwanukan da aka ci abincin, ta d'auki wasu  glass cups kenan message ya shigo wayar ta, ta tsaya dubawa, (da fatar kin tashi lafiya kyakkyawa, wannan shigar da kika yi yau ta dace da kalar fatar ki mai d'aukan hankali, ta 'kara fito da kyakkyawar surar ki, da kuma mumurshi ki mai 'kayatar da kyakkyawar fuskar ki, ina burin jin lallausar muryar ki Minal… Mai 'Kaunar ki). A nan ta saki glass cups d'in duk suka tarwatse, jikin ta ya fara 'kyarma, hakan ya sa Abbah da ummah suka yo kan ta da sauri, Shahid ma da yake waje sai gashi ya shigo da gudu, Abbah ya ce "lafiya? meh yake damunki?" Minal ta shiga jikin shi tana kuka, Abbahan dan Allah ka raba ni da shi, Abbah yace "waye ne Minal?" Tace "Abbah BAN SAN SHI BA, amma Abbah dan Allah ka raba ni da shi ya dame ni , Abbah na a duk inda na shiga yana gani na, komai nake yi ya sani, Abbah na shiga uku aljani ne, Abbah ka ce ya rabu da ni." Abbah ya d'ago ta shima cikin damuwa ya kar6i wayar ta ya duba, ya furzar da iska, yace "Shahid, na baka awa Ashirin da Hudu (24) ka binciko min ko wane d'an iska ne ke bibiyar ‘ya ta, sai na koya masa darasi", ummah tace "Abbahn Minal anya yarinyar nan ba gamo ta yi ba kuwa? Nifa a gani na aljanu ne suke son zautar da ita kawai". Abbah yace "ba wasu aljanu dije, wani d'an iska ne kawai, kuma wallahi sai na yi maganin sa". Shahid yace "Abbah nifa abin ma ya na d'aure min kai wallahi, lambar nan har MTN office naje dan ayi tracing mai wannan lambar amma suka ce ba’a ta6a kira da layin ba, wad'annan sa'konnin da kake gani Abbah, sukad'ai ne ake turawa da layin, kuma a duk lokacin da za’a kira layin sai a ji shi a kashe, ni a gani na ko zancen ummah ne da ta ke cewa aljanu ne, a gwada yi mata rukiyya a gani. Abbah ya d'ago Minal daga jikin sa tana sauke ajiyar zuciya, yace "Minal kin yarda a miki rukiyya?" Tace "Abbah koma menene in dai har zai raba ni da wanna aljanin na yarda a yimin. Nan Hajiya Hadiza ta kira Hajiya Kulu ta ce ta zo da malamin da suka yi magana, ta ce za su zo anjima kad'an. Zancen zuwa skul a nan ya sha 'kasa, aunty Hafsah ce ta bi direban gidan ya wuce da ita, dan Shahid dawowa ya yi ya zauna dan bazai iya fita ba.
Wuraren 'karfe goma shadaya (11) na safe sai ga Hajiya Kulu da ‘yar ta Zainab, da kuma malam mai rukiyya. Suka shigo, Zainab ta je kusa da Minal ta zauna da yake 'kawaye ne, ta fara yi mata sannu tana hayawen tausayin 'kawarta, dan ta san damuwar ta.
Ba tare da 6ata lokaci ba, malam ya saka Minal a gaba ya fara yi mata rukiyya, amma Minal tangaras bata ko yi angaje ba, duk sanda malam ya kira sunan ta, za ta ce masa na’am, har malam ya yi karatun sa ya gama ba alamun aljani a tare da Minal. Malam yace "Alhaji gaskiya wannan karatu da na yiwa Minal, inda aljani ne a tare da ita, da yanzu ya bayyana komai taurin kansa kuwa, amma idan ma aljani ne ke tsorata ta ,toh ba’a jikin ta yake ba, suna so su shafeta ne kawai, ko kuma su cimma wani burin su a kanta" . Nan Minal ta 'kara fashewa da kuka, dan ta tsorata, malam yace "karki damu Minal, zan baki wasu addu’oi ki dage ki dinga karanta su safe da yamma, indai har aljani ne ke bibiyan ki, toh ina tabbatar miki bazai 'kara zuwa kusa da ke ba, idan kuma kika ga babu chanji, toh tabbas shaid'anin mutum ne yake bibiyar ki, bawai aljani ba, sai dai kawai a dage a neme sa". Shahid yace "da kuwa ya ci 'kwal uban sa wallahi ko ma wanne d'an iska ne" . Malam ya rubuta addu’oi ya baiwa Minal, ta kar6a ta fara dubawa, da yake ta yi sauka, karatun larabci baya bata wahala, take ta fara hardace su.
[7/10, 12:51 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
         
          NA
  
  DEEJAH ABDUL 
       💖💞💝
        
        Page  5
Haka dai abin ya ci gaba, Minal ta dage da karatun addu’oin ta, amma abun ba chanji, sai ma 'karuwa da yake, duk ta fita hayyanchinta, hakama iyayenta, duk hankalin su ya tashi, ‘yar gaban goshi ba lafiya. Abbah har ‘yan sanda ya nema ya basu lambar dan amasa bincike, amma babu nasara. Hakan ya sa duk ya 'kwace wayoyin Minal, ya barta da laptop kawai, da yake computer take karatu, hakan ma sai in za ta yi assignment. Amma kuma sai ya zamana ta na samun messeges d'in a facebook account da e-mail d'inta, hakan ya 'kara zautar da Minal, laptop d'in ma ta ajiye bata ta6awa, ko assignment d'in sai dai ta ba yaya Shahid ya mata, ta daina duba komai saboda wannan ba 'karamin razana ta ya yi ba.
Amma duk da haka Minal bata tsira ba, a class idan tana zaune tana lectures idan ta duba takardun ta sai ta samu guntuwar takarda d'auke da sa'kon wannan mutumin wai mai 'kaunarta, haka ko a hanya ta tsaya sai ta samu yaron da zai zo ya mi'ka mata takarda d'auke da sa'kon wannan mutumin, abin har a gida bata da sukuni, a da'kin ta ma ganin takardun ta ke, abin da yafi d'aga mata hankali shine, ita kad'ai ke ganin rubutun, duk lokacin da  aka bata takardar ta duba, kafin ta ba wani ya gani sai rubutun ya 6ace, wannan ya 'kara zautar da Minal, hakan ma iyayen ta sun shiga tashin hankali ba 'karami ba, ganin ‘yar da suke ji da ita wani yana nema ya zautar musu da ita. Hakan ya sa suka dage da neman taimako, malamai kakar su ta yanke sa'ka, dan kuwa zuwa suke da neman bata taimako suna samun na chefane, ga ‘yan sanda suma suna kwasar nasu rabo, amma abun kullum gaba-gaba yake yi. Minal ta koma zautacciya, makaranta ma ta daina zuwa, ta daina kwanciya a d'akinta, kullum tana gurin ummanta da Abban ta, Hajiya Ma’u kuwa ta samu abun murna da farin ciki, ita da ‘yarta kullum cikin habaici da zage-zage, musamman ranar girkin ta idan Abbah ya tare Gun Minal. Ba dan Shahid ba, da kamfanin Abbah ya samu matsala, dan kuwa  yadda Minal ta daina zuwa makaranta, haka shima Abbah ya daina zuwa wajen aiki, dan ba 'karamin so yakewa ‘yar tasa ba, ummah kuwa kullum kuka.