[7/10, 12:58 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 6
Yauma kamar kullum, da yamma duk suna zaune a falo, Minal na kwance kan chinyar ummanta, Nusaiba ce ta shigo ta dawo daga islamiya, sai cewa ta yi, "ke mahaukaciya! ki je waje ana kiran ki", aunty Hafsah tace "wai ke Nusaiba yayar taki kike cewa mahaukaciya dan bakida kunya ko?" Ta maka mata harara kamar manyan idanunta za su zazzago 'kasa, ita kuma ta murgud'a mata d'an 'karamin bakin ta, tace “toh ba mahaukaciyar bace ne? Kullum daga ihu sai kuka", Abbah ya daka mata tsawa “ke fitsararriya wa yake kiran ta a waje? Kuma kika sake kika sake kiran Minal da mahaukaciya sai na 6a66alla ki a gidan nan". Hajiya Ma’u ta jawo ta, “zo nan ‘ya ta kar ya miki illa, zai sauke haushin a kanki, toh ai ba ke kika haukatar musu da ‘yar ba”. Abbah ya sake daka mata tsawa, “wa yake kiran ta na ce?” Ta zun6ure baki, yaya Al-amin ne mana ya zo. Jin hakan ya sa Minal ta mi'ke da sauri ta je d'aki ta d'an gyara fuskarta, ta fito ta yi waje.
Al-amin shi ne saurayin Minal da ta ke so, d'an gidan aminin mahaifinta ne, Alhaji Salisu, wanda suka tashi tare da mahaifin nata tun suna yara, komai a tare suke yi, dan duk 'yan asalin jahar Sokoto ne, kuma yanzu haka kuma a tare suke zaune a Abuja. Har anyi musu baiko da Minal kuma an kawo lefe, jira kawai ake yi Al-amin ya kammala wani course da ya ke yi a Malaysia ya dawo a yi auren su. Yanzu ma hutu ne ya dawo da shi.
Minal ta isa wurin sa da lallausar murmushin ta, duk da ta yi rama ta yamutse kwana biyu, hakan bai hana fitowa da kyaun ta ba, ta isa da sallamar ta, ta ce “What a surprise my hubby, ashe kana gari?” Ya mayar mata da murmushi, babyna jiya na zo, ganin na kasa samun ki a waya, ba chat, ba komai, wannan ne ya d'aga min hankali, ya sa na tattaro na dawo na ga meh ya ke damun masoyiya ta. Minal ta rufe fuska da zara zaran yatsunta, tace "I’m sorry habibinah, dole ce ta sa na ajiye duk wayoyina" , yace "dole kamar ya?" Tace "muje chan garden mu zauna, sai na maka bayanin me yake faruwa" . Suka je suka zauna akan kujerun da ke cikin garden d'in, yace "ina jin ki babyna gayamin dalilin da ya sa kika ajiye wayoyin ki, kikamin mummunan horo na rashin jin sautin ki, da sanin ya lafiyar ki take". Zata fara masa bayani kenan sai aka kira wayar sa, ya d'aga, bayan ya gama wayar ne Minal tace, "wow hobby, muga wayar ka ta burge ni, harda kalarta mai kyau", yace "ko kina so ne na bar miki?" Tace "no sweetheart, waya da kake ganinta ri'keta a gareni ba 'karamin tashin hankali ba ne" . Ta kar6i wayar tashi tana dubawa, sa'ko ne ya shigo a wayar tashi, wanda ya d'aga hankalin Minal, ya sa ta zare ido, wannan ko a mafarki taga wannan lambar zata ganeta, lambar da ke damun ta ce da sa'konni a kowane lokaci, ta mi'ke tsaye jikin ta na 'kyarma, hakan ya sa shima Al-amin ya mi'ke tsaye a rikice, lafiya Minal? Bakin ta na rawa ta ce hobby ina kasan mai wannan lambar? Sa'kon ta bud'e domin ta tabbatar da abinda take zargi. Ga abunda ta gani a ciki, (Zuciya ta tana zafi a duk lokacin da na ganki tare da wani MInal, zuciya ta tana suya a duk lokacin da na ga kina yiwa wani namiji murmushi Minal, Minal ina son ki san cewa ke tawa ce ni kad'ai, bana bu'katar ki tare da kowane d'a namiji. Ki kyaye wannan! Mai 'kaunar ki…). Wani ihu Minal ta saki ta saki wayar Al-amin ta fad'i, take screen d'in wayar ya tarwatse.
[7/10, 1:02 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 7
Al-amin ya du' ka ya d'auki wayar sa, ganin abinda ya sami wayar ya ya harzu'ka.Ke Minal miye haka? Dama da gaske haukan da ake cewa kina yi gaskiya ne? Ji wannan asarar da kikamin Yanzu, kin san ko nawa na siyi wannan wayar da kika fasa min ita? Gashi ba’a ma samun kayan gyaranta a nan yanzu, Minal ta dafe kai tana kuka, “na shiga uku, wayyo Allah na, dan Allah ka rabu da ni, dan Allah dan son iyayen ka ka 'kyale ni, wallahi bana son ka, wallahi na tsane ka, dan Allah ka fita daga rayuwa ta ka barni na zauna lafiya". Al-amin baki bud'e yake kallonta, lallai Minal kin haukace, kuma ni ya kamata na ce na fasa auren ki, dan wallahi bazan iya rayuwa da mahaukaciya ba. Ya juya zai wuce, Minal ta bi bayan shi da gudu, Al-amin ka tsaya ka saurare ni, wallahi ba da kai nake yi ba, da shi nake yi, dan na san yana gani na, kuma yana ji na, da shi nakeyi, wallahi bana son sa, wallahi bana 'kaunar sa, yanzu ya turomin sa'ko a wayar ka, Al-amin ya girgiza kan sa, yace "waye ne Minal?" Tace "BAN SAN SHI BA" . Tsaki ya ja, you are sick Minal, kina bu'katar a kaiki psychiatiric hospital dan a duba 'kwa'kwalwarki dan kin samu ta6in hankali, Allah ya baki lafiya, amma ni bazan iya auren mahaukaciya ba. Ya shiga motar sa ya ja ya barta a nan tsaye tana ruzgar kuka.
Da gudu ta koma cikin gida tana ta kuka ta fad' a kan ummah, tana fad'in "shikenan ummah ya raba ni da Al-amin, Abbah shikenan ya raba ni da Al-amin, Abbah Al-amin ya ce bazai aure ni ba, ka je ka bashi hakuri, Abbah ina son Al-amin bazan iya rabuwa da shi ba". Take zufa ya karyowa Abbah, ya mi'ke ya fara neman wayar Al-amin, Tambayar sa yake yi, me ya ke faruwa tsakanin sa da Minal? Al-amin yace "Abbah gaskiya ku yi hakuri bazan iya auren Minal ba", Abbah cikin tsananin damuwa yace "meh ya sa Al-amin?" Yace "bata gaya muku haukan da tayi min bane Abbah? Gaskiya ni bazan iya auren mahaukaciya ba Abbah, kuje ku nema mata magani kawai". Ran Abbah ba 'karamin 6aci ya yi ba da kalaman Al-amin, amma ganin yanda Minal ke kuka a kan sa, shi ya sa ya dake, yace "toh shikenan zan je in samu Abban ka da zancen dan ba za ku maida mu dattijawan banza ba", ya kashe wayar ya goge gumin da ke goshin sa, yace "Minal daina kuka, yanzu zan je in samu Alhaji Salisu mu yi maganar, Al-amin bai isa ya watsa mana kasa a ido ba". Yace "Shahid ya tashi su tafi gun Alhaji Salisu", ummah da Hafsah ne kawai ke ba Minal ha'kuri akan ta yi shiru komai zai daidaita, yayin da Hajiya Ma’u ke zaune tana tsefewa Nusaiba kan ta, tana ‘yan wa'ke-wa'kenta, a ciki tana jefa musu habaici. Ita ko ja’irar ‘yar tata ta san meh take nufi, sai dariya take kwasa abinta. A haka Hajiya Kulu ta shigo ta same su, ita ma ta zauna tana jajantawa Minal, da zancen Zainab da Shahid ta zo, amma kuma ganin yanayin Minal ya sa ta bar zancen, duk da Zainab d'in ta tabbatar mata dama chan ta dad'e da soyayyar Shahid a zuciyar ta, yawan zuwan da take yi gidan su Minal d'in dama duk dan ta ganshi ne, jin hakan ya 'kara wa mahaifiyarta 'kwarin guiwa, amma ganin matsalar Minal ta san ba wanda zai saurari zancen ta kaf gidan, dole ta ha'kura har zuwa lokacin da hankalin kowa ya kwanta.
[7/10, 1:04 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 8
Abbah kuwa da Shahid sun fita zuwa gidan Alh. Salisu, Suka ci sa’a kuwa yana nan, bayan sun gaisa ne Abbah ya fara magana, Alh. Salisu ya dakatar da shi, “nasan abinda ya kawo ka bai wuce zancen Al-amin da Minal ba, dama tun da dad'ewa nake jin 'kananun maganganu akan ‘yar taka ta samu motsuwa, amma na toshe kunne na tunanin zancen mutane ne kawai, amma yau Aminu ya tabbatarmin da a gabansa ma haukar tata ta tashi, har ta sa shi asarar tsadaddiyar wayar sa, kuma ya tabbatarmin da cewa shi bazai iya auren mahaukaciya ba, kuma Alhaji Abbah kafi kowa sanin hali na, kasan a tsari na ba matsawa a rayuwar ‘ya’ya na, dan haka na goyi bayan Aminu, kawai kaje ka nemawa ‘yarka magani, Allah Ubangiji Ya bata lafiya. Ba Abbah ba, har Shahid wad'annan maganganu sunyi matu'kar 6ata masa rai, Shahid ya mi'ke a fusace yace "Abbah tashi mu tafi, ai wannan chin fuska ne. Abbah ya mi'ke jiki a sabule, yace "Alh. Salisu kwata-kwata ban yi tunanin haka daga wurinka ba, na dauka zumunci da 'kaunar da take tsakanin mu ta wuce komai, ko da gaske ne ‘yata hauka take, ban d'auka kana d'aya daga cikin mutanen da za su guje ni da iyali na ba". Nan mahaifiyar Al-amin Haj. Saratu da take la6e tana jin abinda ake yi, sai ko ta yi kutsul ta fito, tace, “Alhaji mu sai mu rufawa ‘yar taku asiri mu chutar da namu yaron? Sanin kan ka ne zaman mai hankali da ta6a66e ba abune mai yuwa ba, ranar da haukar tata ta tashi Allah kaid'ai ya san abinda zata masa, toh mu gaskiya ba zamu yarda ba, dole ne a fasa wannan aure”. Alhaji Salisu ya mi'ke, “Kayi ha'kuri Alhaji Abbah, amma ni a gaskiya ban had'a komai da farin cikin ‘ya’ya na ba, dan haka bazan tilasta yaro na auren mahaukaciya ba”. Wani zugi Abbah ya ke ji a zuciyar sa a duk lokacin da aka kira Minal d'insa da mahaukaciya, hakan ya sa Abbah ya 'kara harzu'ka ya d'agawa Alh. Salisu hannu, cikin tsawa yace, "nagode Allah da ya nuna min irin 'kaunar da kake min a yau, nagode Allah da ban aurar da ‘yata a wurin da ba za’a iya tsaya mata ba komai ya same ta, Alh. Salisu ina so ka san wani abu, daga yau zumuncin da yake tsakanin mu ya 'kare, ba wai ina nufin na huld' ar da ta ke tsakanin 'ya'yanmu ba kawai, a'ah dangantaka komai, ta kasuwanci da duk wata mu'amala da take shiga tsakanina da kai da iyalina, yanda kace ba zaka tilasta 'ya'yanka ka chutar da su ba, haka nima ba zaka 'kara ra6ata ba, dan ban yarda dakai ba, dangantakar da take tsakaninmu tin kan musan zamu sami wasu 'ya'ya a duniya ta 'kare daga yau, dan nima bazan iya zama da ma'kiyi na ba, kuma ma'kiyin iyalina, bazan iya huld'a da wanda yake gudun had'a zuri'a dani ba, kawai dan wata lalura ta sami 'yata, kuma minal ba hauka take ba, wata lalura ce ta had'u da ita, kuma soon inshaAllahu zamuyi maganinta, koda kuwa duk abunda na mallaka a duniya zai 'kare", ya juya fuuuu ya fice, alhj salisu ji yake kamar ya ruga da gudu ya kamoshi ya bashi ha'kuri, amma yana gudun yayi abun kunya a gaban iyalinsa, tabbas yasan rashin alhj abbah a harkokinsa ba 'karamar asara zai tafka ba, dan alhj abba ya toshe masa 'kofofi da dama, amma yanzu bari ya barshi, daga baya ya bishi ya lalla6ashi su daidaita.
[7/11, 8:43 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 9
Alhj abba da shahid na fita hjy saratu itama ta kwashi direba ta nufi gidan su minal d'in tana zage-zage, tana fad'in dole ne naje na kwaso dukiyar d'ana da take gidan, kwandala bazan barmusu ba, zan nuna musu ba sai dasu zamu iya rayuwa ba, alhj slisu shidai jinta kawai yake, dan yasan da bazar alhj abba yake taka rawa.
Tun a hanya abbah yace "shahid na baka dama duk wata share (hannun jari) da kasani da sunan alhj salisu a kamfanina kasakasu a kasuwa ka siyar da su, dama ai duk ni na siya masa su, amma wlh daga yau ta 'kare ba ni ba shi", shahid yace "angama abbah, dama ni na tsani mutumen wlh, zai gane shi ba komai bane" da haka suka isa gida ko wannen su huci yake kmar tsohon kumurci kan tsananin 6acin rai. Minal tana ganinsu ta taso da gudu tayo wurin abbah tana fad'in "abbana al'amin ya hakura ko? Abbana al'amin bai fasa aurena ba ko?" abba yayi shiru hawayen ba'kinciki ne suka zubo masa ba tareda ya sani ba, yayi sauri ya share, ya bud'e baki zaiyi magana kenan, sai ga hjy saratu ta fad'o gidan ba ko sallamah, hakan yasa ummah da hjy kulu suka mi'ke tsaye cikin hanzari, hjy kulu tace "haba hjy saratu, ai dai ko da meh kika zo bai dace ki fad'owa mutane gida ba ko sallamah ba", bud'ar bakinta sai cewa tayi "SALLAMAH AI ADDU'AR NEMAN AMINCI CE, NI KUMA BA AMINCIN NE YA KAWO NI BA" baki suka saki suna kallonta cikin mamaki, tace "ba tare da 6ata lokaci ba inason a tattaromin duk wani Abu da kukasan d'ana ya kawowa wannan mahaukaciyar yarinyar, wlh 'kwandala kuka 6oye bamu yafe ba", take minal ta gano abunda ke faruwa, cikin sauri taje ta du'ka gun hjy saratu tace "momy dan Allah kuyi hakuri karku rabani da al'amin" wata dalleliyar harara ta mako mata, tareda cewa " ki d'aga ki bani wuri kar na hankad'eki, yarona bazai auri mahaukaciya ba wlh, saidai mu nemo masa dalleliya mai kyau da lfy ya aura amma ba ke ba" ummah ranta yakai 'kololuwar 6aci tazo ta d'ago minal daga 'kafafun hjy saratu, minal ta fara tirjewa tana kuka, ummah ta daka mata uwar tsawa take ta nutsu, tace " hjy kulu muje ki tayani kwaso kayan, hafsah ma ta bisu, take suka kwaso kayan lefen minal da duk wani abu da suka San al'amin ne ya siyowa minal suka jibge mata, handkerchief wannan idan hfsh ta gayawa umma na al'amin sai an ciro shi, hjy saratu ta shiga binciken kayan taga wai koda an cire wani abun, ammma ga mamakinta komai yananan kamar yanda aka kawo, kayan gani ma tayi kamar 'karosu akayi.
'dago kanta da zatayi nusaibah ta watso mata kayan chocolate d'inda al'amin d'inne yake kawo mata idan yazo, harda juices, wani kwalin ma har ta fasashi duk ya tarwatse a jikin hjy saratu, Baki bud'e hjy saratu ke kallon nusaiba, ita kuma ta ri'ke kwankwaso tana jijjiga, tace " hajiya ga tsiyarku nan ku kwashe ku tafi, yayata zata iya zama mahaukaciya amma kunsan cewa dubun wannan kayan munfi 'karfinsu, Allah na tuba ai duk munsani ma da kud'in abbanmu aka siyi kayan, ko mijinki ba a wurin abbnmu yake maula ba? Amma dukda haka mu ba matsiyata bane ku kwasa ku tafi, idan ma banda kaddara meh aunty minal zatayi da yaya al' amin? Keda ganin fuskarsa ma kinsan shaye-shaye yake, kuma kowa ya sani d'an iska ne mata yake bi, nasha ji mommy na tana fad'a amma nayi shiru dan tace kar na fad'a, amma yau ya zama dole na fad'a dan bazaiyu ki shigo har cikin gidanmu ki ci mana mutunci ba, dan haka ga gayyar tsiyarku nan ku kwasa, ta fara d'ibar kayan tana wurgawa a waje, wasu ma 'kafa take sakawa tana ball da su, duk da tsanar rashin kunya da rashin mutuncin nusaiba da kowa yayi, yau ba wanda yayi 'ko'karin hanata, sai ma murna da sukayi yau ta tsayawa 'yar uwarta, ashe dai kowa da ranarsa, ko marasa mutunci ma da ranarsu, hjy saratu duk rashin mutunci da ta zo dashi, sai gashi tayi mus, mamaki ya kasheta yanda 'yar 'kan'kanuwar yarinya ta mata tatas ta kasa cewa komai, a haka cikin borin kunya ta kwashi kayan ta fita.
[7/11, 10:20 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL ,
💖💞💝
Ban yarda wani ko wata ya kwashe ko ya juyamin da labari ta kowacce irin hanya ba, duk wanda yayi haka wallahi Allah ya isa, ban yafe masa ba, kuma ko meh na masa shi ya ja wa kansa.
Page 10
Tana fita hjy ma'u ta kwashe da dariya, Ana cewa 'yata 'yar iska ce, mara mutunci yau gashi ta tsayawa mahaukaciyar 'yarku, meh yasa yau ba wanda ya kwa6eta?ke zo nan nusi na er albarka, taje da gudu gun mamanta tana dariya, yau tayi abun kirki har abbah bai mata tsawar da ya saba ba. Hajiya ma'u ta ci gaba " kuma mudai kaf danginmu ba muyi gadon mahaukata ba, bamuda mahaukaci ko d'aya saidai ko idan achan ta d'auko, ummah maganar ta mata zafi dan tasan da ita take yi, ta mi'ke tace " ma'u meh kike nufi? Kina nufin a dangina kenan minal tayi gadon hauka kenan? Tinda dai nice bare a cikinku, ma'u tayi dariya tace " kinji na ambaci sunanki hadiza? Dama dai ance mai kaza a aljihu baya jimirin asss". Abbah dai zuciyarsa a chunkushe take yama kasa che musu komai, ga uban kukan da minal take yi da yake 'kara 'kona masa zuciya.
Shahid ne yazo gun minal d'in ya du'ka yace " 'kanwata kalleni, ta d'aga idonta da sukayi jajir ta kalleshi, yace ki daina kuka, ke ba mahaukaciya bace, munsan kinada hankalinki, kuma zamuyi maganin matsalarki inshaAllah, kuma ki daina d'aga hankalinki akan al'amin, Sam bai dace da ke ba, kuma baya 'kaunarki, dan idan yana sonki da gaskiya minal duk halin da kika shiga bazai guje ki ba, masoyin gaskiya baya gudun masoyinsa duk tsanani duk wuya, dan haka ki yrda al'amin baya sonki ki daina 6ata hawayenki akan shi, wani hanin ga Allah baiwa ne, kina zaune zaki ga Allah ya Miki sauyi da mafi alkhairi, mai sonki da gaskiya, ki dage da addu'a kawai kinji 'kanwata? Gyad'a masa kai tayi tareda murmushi dan tasan gaskiya ya gayamata, ta d'ago tace " abbah ummah, kuyi hakuri na d'aga muku hankali, nasa anci mutuncinku, inshaAllah zanyi iya kokarina naga na cire al' amin daga zuciyata" . Abbah ya sauke wata ajiyar zuciya ya dafa kafad'ar shahid, dan yasan maganganunsa ne suka sa minal ta ha'kura, yace " yace thanks son, ka tashi ku fita da 'kannenka ku zaga gari, kuje shopping da shan ice cream, Nusaibah ta taso, abbah nima dani za'aje shan ice cream d'in ko? Tinda dai yau nayi abun kirki, dariya abbah yayi kawai yace " je ki shirya 'yar momynta, kema aje da ke, suka tashi sukayi ciki domin su shirya, shima abbah yace zaije ya d'an watsa ruwa ya huta, ya wuce ciki.
Hajiya kulu ta dubi hajy hadiza tace " ni ko hjy hadiza anya ba hannun kishiyarki a lamarin minal? Ki duba fa kiga, 'karara take nuna farincikinta akan abunda yake faruwa akan minal, hjy hadiza tace " hmmm kulu kenan, nasan ma'u sarai, nasan abunda zata iya da wanda ba zata iya ba, nasan ta tsani yanda taga abban minal yake sonta, amma kuma bata 6oye tsanarata da hasadarta, a bayyane take komai nata, ita dai ki barta da habaice-habaice, amma gaskiya bana tunanin wai da sa hannunta a lalurar minal, kuma kinji annabin rahma yace " AZZANU ZAMBUN WALAU KANA HAKKUN (ZATO ZUNUBI NE KO DA YA ZAMA GASKIYA)" dan haka wlh har ga Allah bana zarginta, duk wani wanda yake nufinmu da sharri ina ro'kon Allah da ya mayar masa da mugun nufinsa, hjy kulu tace " amin, amma gaskiya hadiza zuciyarki tanada kyau, Allah yasa mu dace" , ta mi'ke da niyar tafiya, hjy hadiza tace hajiya kulu kar kiga kamar na 'kyale zancen shahida da zainab, Wallahi ba mantawa nayi ba, matsalar nan ce ta minal ta samu a gaba, amma inshaAllah da komai ya lafa zan shigo da zancen", hjy kulu tace " karki damu kanki hadiza, Wallahi na fahimta, Allah dai yasa mu dace". Sukayi sallamah ta fita.
No comments:
Post a Comment