[7/10, 12:00 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 1
Tafe take cikin sauri tana waigen bayan ta, karar shigowar sa'kon waya da ta ji, shi ya kara sa hankalin ta ya tashi. Tsayawa ta yi, hannu na kyarma ta bude sa'kon, take kanta ya buga ta kuma kara firgita. Ga abunda ta gani a ciki (ki tsaya ki yi tafiyar ki tsaf mai daukar hankali, bana gajiya da kallon ki, ki daina takun sauri kada ki illatamin kan ki, kar ki manta, a duk inda kike, ina tare da ke. MAI 'KAUNAR KI… Hannunta ta dora a kai zata 'kurma ihu, yaya Shahid ne ya daka mata tsawa, WAI KE WACE IRIN MAHAUKACIYA CE MINAL? Tun dazu nake bibiyar ki a baya ina miki horn amma sai zabga uban sauri kike, anya Minal wannan rayuwar zata fishshe ki kuwa? Hannu ta dora a kai, yaya na shiga uku, Wallahi aljani ne, duk inda na shiga sai ya bini, komai nake yi yana gani na, kuka take ba tsayawa harda tsalle, kuma wallahi yaya BAN SAN SHI BA. Yaya Shahid ya ja dogon tsaki, wai wannan wace irin rayuwa ce? Bana gaya miki ki chanja layi ba? Tace wallahi yaya wannan na bakwai ke nan, shiru ya yi, Bani number din na kira, kira yake a kasha, wani sabon kukan ta dasa, yaya kullum number a kashe amma kuma kullum sai an yi min text da ita. Yaya Shahid yace yi shiru haka Minal, zo mu tafi gida. Ya ja hanunta ya saka a mota ya na girgiza kai, wannan waye yake nema ya zautar masa da ‘yar kanwar sa? Koma waye za suyi maganin sa.
WACECE MINAL?
Suna na Aminah Abbah Khaleel, amma anfi kira na da Minal Abbah Khaleel, yayin da qawaye na da classmates dina suke kira na da Minal Abbah kawai. Mahaifi na dan asalin jihar Sokoto ne, amma aiki ya kai shi birnin tarayya (Abuja) inda muke zaune. Mahaifiyata sunan ta Hajiya Hadiza, ni kad'ai ta Haifa, daga nan haihuwa ta tsaya mata, Wannan ne ya sa dangin mahaifina suka tilasta Abbahna ya auro ‘yar uwarsa, Hajiya Asm’au wacce ita ma Nusaiba kawai ta haifa daga nan haihuwa ta tsaya mata, hakan ya sa mutane suka dinga cewa abun daga abbanmu ne, kowace mace ya auro daga ta haihu d'aya kuma shikenan, gashi baya da magaji, wai tinda bayada d'a namiji. Shekara bakwai ne tsakani na da Nusaiba, yanzu ina matakin farko ne a jami’ar Abuja (100 level) inda nake karatun ilimin kimiyya na na’ura mai kwakwalwa (Computer Science) yayin da Nusaiba take aji daya na karamar sakandare (JSSI).
WAYE SHAHID?
Yaya Shahid d'an 'kanen mahaifina ne, da yake mahaifin su bai yi wani zurfi a karatun boko ba, ya riga mahaifi na aure, shiyasa duk 'ya 'yansa suka girmemu, yaya shahid ne babba shekarunsa ashirin da bakwai yanzu a duniya, yana aiki ne a kamfanin abbah na, shi yake kula masa da dukkan dukiyoyinsa, yayinda aunty hafsah take bi mishi, itama tana matakin 'karshe ne a jami'ar abuja, yayinda take karanta mass communication.
Mahaifinsu shahid 6ata yayi ba' a san inda yake ba, annemishi a ko'ina an rasa, tin yaya shahid nada shekara goma sha bakwai a duniya, wannan ne yayi sanadiyar sakawa mahaifiyarsu hawan jini har ta rasa ranta, daga lokacin ri'konsu ya dawo hannun abbanmu.
[7/10, 12:39 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 2
CIGABAN LABARI
A hargitse ta shiga gidan su, mahaifiyar ta Hajiya Hadiza da kawarta Hajiya Kulu suna zaune a falo suna fira, Minal ta fad'o falon kamar wadda aka koro ba ko sallama, da gudu ta wuce d'akin ta tana kuka, Hajiya Kulu ta kalli Hajiya Hadiza ta ce me ke faruwa da Minal ne? Yarinya mai nutsuwa da hankali amma yau ta shigo gida ba ko sallama, kuma ko ta gaida mu? Kuma na lura da bawai dan bata ganmu bane, Kafin Hajiya Hadiza ta yi magana sai ga Shahid ya shigo da sallamar sa, suka karba masa, ya rusuna ya gaida su, Ummah tace niko Shahid me ke damun kanwar taka ne? Ya dukar da kansa cikin nutsuwa ya fara magana. Ummah wallahi matsalar bata wuce wa’yannan sakonni da take samu a wayar ta ba kullum, kuma ta rasa gane waye, ni kaina bincike nake amma na kasa gane ko waye, amma wallahi ummah ko ma waye na yi alkawarin duk ranar da dubun sa ta cika sai ya raina kanshi. Hajiya Kulu ta ce niko Hajiya Hadiza anya yarinyar nan ba gamo ta yi ba kuwa? Tun lokacin da kika gayamin matsalar yarinyar nan kuma na yi nazari sai naga kamar aljanu ne kawai ke son wasa da hankalin ta. Amma ki bari zan yi ma wani malamin su Zainab magana naga yana rukiyya, sai ya zo ya mata. Hajiya Hadiza cike da tsananin damuwar abinda ke damun ‘yar ta kwaya daya tilo, ta ce bakomai Hajiya Kulu, Ki yi masa magana kawai, ni kaina matsalar yarinyar nan a kullum da ita nake kwana nake tashi, da chan na yadda da zancen mahaifin ta da yake cewa shirmen ta ne kawai mu kyale ta, Amma yanzu lurar da na yi yarinyar nan ba ta da sukuni a ‘yan kwanakin nan ya sa nima na fara shiga damuwa. Shahida ne ya mike ya ce ummah ni zan fita, ta ce toh ka dauki abincin ka gashi nan a kan dining, ya je ya dauka cikin girmamawa ya musu sallamah ya fita. Hajiya Kulu ta ce niko Hajiya Hadiza da za ki yadda da mun hada zumunci, auren Shahid da Zainab ta wuri na, dan yaron natsuwar sa ta yi min, na yaba da hankalin sa. Hajiya Hadiza ta ce duk da yaran zamanin nan, ba'a musu katsalandan a rayuwa, yaronnan ba ni na haife shi ba, amma na yar da da shi da natsuwar sa, yana ban girma tamkar ni na tsuguna na haifeshi, na tabbata bazai watsa mana 'kasa a ido ba, karki damu zanyi masa maganar. Hajiya Kulu ta mike ta ce zata tafi, tare da ro'kon Hajiya Hadiza da ta yi ma Shahid zancen Zainab, Nan suka yi sallamah ta tafi a kan za ta zo da mai rukiyya zuwa gobe.
Minal kuwa tun da ta fad' a d'akinta maida 'kofa ta rufe tana kuka, da ta gaji ta yi shiru dan kan ta, har wani wahallalen bacci ya yi gaba da ita, Ranar dai a ta' kaice bata bud'e 'kofar d' akin ta ba, ko abinci bata samu damar ci ba, Ummah da Aunty Hafsah sunyi-sunyi da ita ta bud'e kofar, ta'ki, Dole suka ha'kura suka 'kyale ta.
[7/10, 12:41 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 3
Tun bayan ta yi sallar asuba ta tsaya tana azkar na safe da karatun Al-Qurani, ta du' kufa da addu’a na Allah Ya shiga tsakanin ta da ma kowaye ke son ya zautar da ita, domin tun abin baya damun ta, yanzu ya hana ta sukuni. Bayan ta gama ne ta tashi ta shiga wanka ta fara shiri domin tana da lecture wanna ranar. Ta gama shirn ta tsaf, ta d'auko kayan ta ta fito waje, ta samu iyayen ta Alh. Abbah Khaleel, Hajiya Hadiza, da Hajiya Asma’u, Nusaiba kuma tana gefe, yaya Shahid da aunty Hafsah, duk suna kan dininig suna karyawa. Ta matsa ta gaida kowa cikin fara’a suma kowa ya kar'ba mata da fara’a. Abbah ya ce Minal d'in abban ta zonan kusa da ni ki zauna, ta je kusa da shi ta zauna tamkar ta shige jikin sa, Hakan ya sa Hajiya Asma’u ta ja wani gwauron tsaki, dan ta tsani yanda Alhaji yake nuna ya fi son Minal a kan ‘yar ta Nusaiba. Ba wanda ya kulata, domin idan da sabo, kowa ya saba dan halin ta. Abbah ya ci gaba, Minal d'ina shine jiya kika ki fitowa ki gaida ni ko? Ummahn ki ta gaya min tunda kika dawo makaranta baki fito ba, Ta ce ba komai Abbah na, kawai bana jin dad'i ne. Abbah ya ce, "kin san kuwa rashin ganin ki nima da zazzabi na kwana ko?" Hakan ya sa kowa ya yi dariya. Hajiya Hadiza ta ce "haba Alhaji ka daina fad'in haka mana" . Abbah da kan sa ya zuba ma Minal abin kari, ya ce Minal din Abbahnta ci abincin ki kar ki kula da umman ki, kishi ne yake damun ta. Hajiya Asma’u ta mi'ke tana sabbatu, haba! mutum kullum sai biyewa 'karamar yarinya, idan wani bai san ‘yarka bace ai ace wannan karuwarka ce, haba, son ‘ya hauka ne? A gaban ‘ya’yanka ka dage kana wani tarairiyar yarinya kamar ‘yar goye? Ta ce wa Nusaiba tashi muje direba ya wuce da ke autata, ko ba’a son ki dole ne a ganki. Nusaiba ta mi'ke zata wuce, Abbah ya daka mata tsawa, KE DAWO NAN KI KARASA BREAKFAST DINKI!!! Idan kika d'aga daga nan sai na 6alla ki. Ta dawo ta zauna tana zum6ura baki, daddy tunda ni baka son gani na ai gwanda na tafi, Shahid ne ya buge mata baki, ke gaki ‘yar 'karama se shegiyar tsiwar tsiya. Hajiya Ma’u ta 'kufula dan Alhaji da Hajiya Hadiza da ta so su kula ta, ba wanda ya kula ta, sai ta fara saukewa a kan Shahid, ta zage shi tatas. Kai d'an ri'ko ka zo ka fi masu gida sakewa harda dukan ‘yar masu gida, Aunty Hafsah ta je ta maida mata amsa, Shahid ya d'aga mata hannu akan ta yi shiru ta 'kyale ta. Abbah ne ya mi' ke, Ma’u duk tsiyan da za ki yi zan iya 'kyale ki, amma bana son kina ta6a min yarana, Shahid da Hafsah da Minal da Nusaiba, duk d'aya suke a wuri na ba babanci, ‘ya’yan d'an uwana ne, uwa d'aya uba d'aya, dan haka ba suda bambanci da ‘ya’yan ciki na. Ke a kullum burin ki bai fi ki ga kin raba min kan ‘ya'yana ba, ‘yar ki da kike fad'in ba’a son ta, ki yi 'ko' kari ki koya mata tarbiyya, ita ce 'karama a gidannan amma rashin kunyar ta ya girmi kowa a gidannan, kuma duk lokacin da za’a yi mata fad'a ko a kwa6eta, bakya so a ta6a ta, to iya ‘yar gwal ce da ba za’a yi mata fad'a ba? Duk nawa Nusaiba take? Amma bata ganin girman kowa. Toh ya kamata ki chanja hali dan ki koyawa ‘yar ki tarbiyya yanda za ta girmama na gaba da ita, sannan sai a so ta. Nusaiba ce ta mi'ke, Mommyna mai so na muje nagama, na kuma gaji da jin Abbah yana miki ihu kamar wata 'karamar yarinya, kodai a so mu ko kada a so mu dole ne a ganmu, ba yanda za’a yi da mu, ita ‘yar da aka fi so ai gashi nan neman haukacewa take. Minal ta mi'ke a fusace zata janyo Nusaiba, Nusaiba ta ruga da gudu ta fita gidan. Hajiya Ma’u ta yi murmushi, na gode Allah da Ya ban ‘ya mai hankali, tun tana 'karama bata son ta ga ana cin zarafin mahaifiyar ta, ta wuce ta barsu da mamaki. Abinda Nusaiba ke yi ba wanda zai ce wai shekara goma ce, rashin kunyar ta bata ragawa kowa, har uwar tata idan ta tashi sai ta mata tas.
[7/10, 12:50 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 4
Shahid ne ya katse shirun da cewa " 'kanawata idan kun gama ku same ni a waje na sauke ku a makaranta" . Ya mi'ke ya fita, aunty Hafsah ma ta mi' ke ta yiwa su ummah sallama, Minal ma ta gama, sai ta tsaya tana kwashe kwanukan da aka ci abincin, ta d'auki wasu glass cups kenan message ya shigo wayar ta, ta tsaya dubawa, (da fatar kin tashi lafiya kyakkyawa, wannan shigar da kika yi yau ta dace da kalar fatar ki mai d'aukan hankali, ta 'kara fito da kyakkyawar surar ki, da kuma mumurshi ki mai 'kayatar da kyakkyawar fuskar ki, ina burin jin lallausar muryar ki Minal… Mai 'Kaunar ki). A nan ta saki glass cups d'in duk suka tarwatse, jikin ta ya fara 'kyarma, hakan ya sa Abbah da ummah suka yo kan ta da sauri, Shahid ma da yake waje sai gashi ya shigo da gudu, Abbah ya ce "lafiya? meh yake damunki?" Minal ta shiga jikin shi tana kuka, Abbahan dan Allah ka raba ni da shi, Abbah yace "waye ne Minal?" Tace "Abbah BAN SAN SHI BA, amma Abbah dan Allah ka raba ni da shi ya dame ni , Abbah na a duk inda na shiga yana gani na, komai nake yi ya sani, Abbah na shiga uku aljani ne, Abbah ka ce ya rabu da ni." Abbah ya d'ago ta shima cikin damuwa ya kar6i wayar ta ya duba, ya furzar da iska, yace "Shahid, na baka awa Ashirin da Hudu (24) ka binciko min ko wane d'an iska ne ke bibiyar ‘ya ta, sai na koya masa darasi", ummah tace "Abbahn Minal anya yarinyar nan ba gamo ta yi ba kuwa? Nifa a gani na aljanu ne suke son zautar da ita kawai". Abbah yace "ba wasu aljanu dije, wani d'an iska ne kawai, kuma wallahi sai na yi maganin sa". Shahid yace "Abbah nifa abin ma ya na d'aure min kai wallahi, lambar nan har MTN office naje dan ayi tracing mai wannan lambar amma suka ce ba’a ta6a kira da layin ba, wad'annan sa'konnin da kake gani Abbah, sukad'ai ne ake turawa da layin, kuma a duk lokacin da za’a kira layin sai a ji shi a kashe, ni a gani na ko zancen ummah ne da ta ke cewa aljanu ne, a gwada yi mata rukiyya a gani. Abbah ya d'ago Minal daga jikin sa tana sauke ajiyar zuciya, yace "Minal kin yarda a miki rukiyya?" Tace "Abbah koma menene in dai har zai raba ni da wanna aljanin na yarda a yimin. Nan Hajiya Hadiza ta kira Hajiya Kulu ta ce ta zo da malamin da suka yi magana, ta ce za su zo anjima kad'an. Zancen zuwa skul a nan ya sha 'kasa, aunty Hafsah ce ta bi direban gidan ya wuce da ita, dan Shahid dawowa ya yi ya zauna dan bazai iya fita ba.
Wuraren 'karfe goma shadaya (11) na safe sai ga Hajiya Kulu da ‘yar ta Zainab, da kuma malam mai rukiyya. Suka shigo, Zainab ta je kusa da Minal ta zauna da yake 'kawaye ne, ta fara yi mata sannu tana hayawen tausayin 'kawarta, dan ta san damuwar ta.
Ba tare da 6ata lokaci ba, malam ya saka Minal a gaba ya fara yi mata rukiyya, amma Minal tangaras bata ko yi angaje ba, duk sanda malam ya kira sunan ta, za ta ce masa na’am, har malam ya yi karatun sa ya gama ba alamun aljani a tare da Minal. Malam yace "Alhaji gaskiya wannan karatu da na yiwa Minal, inda aljani ne a tare da ita, da yanzu ya bayyana komai taurin kansa kuwa, amma idan ma aljani ne ke tsorata ta ,toh ba’a jikin ta yake ba, suna so su shafeta ne kawai, ko kuma su cimma wani burin su a kanta" . Nan Minal ta 'kara fashewa da kuka, dan ta tsorata, malam yace "karki damu Minal, zan baki wasu addu’oi ki dage ki dinga karanta su safe da yamma, indai har aljani ne ke bibiyan ki, toh ina tabbatar miki bazai 'kara zuwa kusa da ke ba, idan kuma kika ga babu chanji, toh tabbas shaid'anin mutum ne yake bibiyar ki, bawai aljani ba, sai dai kawai a dage a neme sa". Shahid yace "da kuwa ya ci 'kwal uban sa wallahi ko ma wanne d'an iska ne" . Malam ya rubuta addu’oi ya baiwa Minal, ta kar6a ta fara dubawa, da yake ta yi sauka, karatun larabci baya bata wahala, take ta fara hardace su.
[7/10, 12:51 PM] Deejah Abdul🌺🌸🌺: BAN SAN SHI BA
NA
DEEJAH ABDUL
💖💞💝
Page 5
Haka dai abin ya ci gaba, Minal ta dage da karatun addu’oin ta, amma abun ba chanji, sai ma 'karuwa da yake, duk ta fita hayyanchinta, hakama iyayenta, duk hankalin su ya tashi, ‘yar gaban goshi ba lafiya. Abbah har ‘yan sanda ya nema ya basu lambar dan amasa bincike, amma babu nasara. Hakan ya sa duk ya 'kwace wayoyin Minal, ya barta da laptop kawai, da yake computer take karatu, hakan ma sai in za ta yi assignment. Amma kuma sai ya zamana ta na samun messeges d'in a facebook account da e-mail d'inta, hakan ya 'kara zautar da Minal, laptop d'in ma ta ajiye bata ta6awa, ko assignment d'in sai dai ta ba yaya Shahid ya mata, ta daina duba komai saboda wannan ba 'karamin razana ta ya yi ba.
Amma duk da haka Minal bata tsira ba, a class idan tana zaune tana lectures idan ta duba takardun ta sai ta samu guntuwar takarda d'auke da sa'kon wannan mutumin wai mai 'kaunarta, haka ko a hanya ta tsaya sai ta samu yaron da zai zo ya mi'ka mata takarda d'auke da sa'kon wannan mutumin, abin har a gida bata da sukuni, a da'kin ta ma ganin takardun ta ke, abin da yafi d'aga mata hankali shine, ita kad'ai ke ganin rubutun, duk lokacin da aka bata takardar ta duba, kafin ta ba wani ya gani sai rubutun ya 6ace, wannan ya 'kara zautar da Minal, hakan ma iyayen ta sun shiga tashin hankali ba 'karami ba, ganin ‘yar da suke ji da ita wani yana nema ya zautar musu da ita. Hakan ya sa suka dage da neman taimako, malamai kakar su ta yanke sa'ka, dan kuwa zuwa suke da neman bata taimako suna samun na chefane, ga ‘yan sanda suma suna kwasar nasu rabo, amma abun kullum gaba-gaba yake yi. Minal ta koma zautacciya, makaranta ma ta daina zuwa, ta daina kwanciya a d'akinta, kullum tana gurin ummanta da Abban ta, Hajiya Ma’u kuwa ta samu abun murna da farin ciki, ita da ‘yarta kullum cikin habaici da zage-zage, musamman ranar girkin ta idan Abbah ya tare Gun Minal. Ba dan Shahid ba, da kamfanin Abbah ya samu matsala, dan kuwa yadda Minal ta daina zuwa makaranta, haka shima Abbah ya daina zuwa wajen aiki, dan ba 'karamin so yakewa ‘yar tasa ba, ummah kuwa kullum kuka.
No comments:
Post a Comment